IQNA

19:49 - April 12, 2021
Lambar Labari: 3485800
Tehran (IQNA) babban malamin cibiyar Azhar ya mika sakon taya murna ga dukkanin musulmi dangane da zagayowar watan ramadan mai alfarma.

Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, Sheikh Ahmad Tayyib babban malamin cibiyar Azhar ya mika sakon taya murna ga dukkanin musulmi dangane da zagayowar watan ramadan mai alfarma na wannan shekara.

Malamin ya bayyana a shafinsa an twitter cewa, yana mika sakon taya murna ga dukkanin musulmi na duniya baki daya, dangane da zagayowar wannan lokaci mai albarka.

Ya ce lokaci ne da ya kamata musulmi su yi amfani da shi wajen yawaita ibada ga Allah madaukakin sarki, da kuma nisantar dukkanin abubuwan da Allah ya hana aikata su.

Darul Ifta a kasar Masar wadda ita ce babbar cibiya mai bayar da fatawar musulunci ta sanar da cewa, a jiya Lahadi ba a samu ganin watan Ramadan ba a kasar, saboda haka ranar gobe talata ce 1 ga watan ramadan.

 

3963871

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: