IQNA

Karatun Kur’ani Ga Wadanda Suka Yi Shahada Wajen Kare Quds

23:46 - April 17, 2021
Lambar Labari: 3485817
Tehran (IQNA) ofishin Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya bude wani shiri na karatun kur’ani ga dukkanin wadanda suka rasa rayukansu wajen kare Quds.

Ofishin kula da rubuce-rubuce na Ayatollah Sayyid Ali Khamenei jagoran juyin juya halin muslunci a kasar Iran, ya bude wani shiri a shafin KHAMENEI.IR  na karatun kur’ani ga dukkanin wadanda suka rasa rayukansu wajen kare Quds, shirin kuma yana gudana nea  cikin wannan wata na ramadan.

Manufar wannan shiri dai ita ce tunawa da dukkanin wadanda suka sadaukar da rayuwarsu domin kare martabar masallacin Quds alkiblar musulmi ta farko, tare da girmama su da kuma girmama sadaukarwar da suka yi.

Bayanin ya ce akwai mutane masu yawa ad suka yi sadaukarwa saboda Quds a duniya, baya ga Falastinawa da suke gwagwarmaya wajen kalubalantar yahudawa da suke mamaye da wannan masallaci mai alfarma..

 

 

3964981

 

captcha