IQNA

Kamfe Mai Taken (Falastinu Ba Ita Kadai Take Ba) Domin Nuna Goyon Baya Al'ummar Birnin Quds

23:39 - May 01, 2021
Lambar Labari: 3485865
Tehran (IQNA) an bude wani kamfe da baje koli mai taken Falastinu ba ita kadai take ba da nufin nuna goyon baya ga al'ummar Falastinu da kuma kare masallacin Quds.

An fara gudanar da wani kamfe da kuma baje koli a birnin Tehran, mai taken Falastinu ba ita kadai take ba da nufin nuna goyon baya ga al'ummar Falastinu da kuma kare masallacin Quds mai alfarma, wanda Mas'ud Shojaei Tabataba'i ke jagoranta, tare da nuna kayayyaki fiye da 3000 daga kasashe 66, da suke nuna abubuwa da suka shafi Falastinu da birnin Quds.

 

3967566

 

captcha