IQNA

Saudiyya: Maniyyata Dubu 60 Ne Kawai Za Su Sauke Farali A Shekarar Bana

22:54 - June 12, 2021
Lambar Labari: 3486003
Tehran (IQNA) Mahukuntan kasar Saudiyya sun sanar da cewa, maniyyata dubu 60 kawai za su samu damar sauke farali a shekarar bana.

A yau ma’aikatar kula da ayyukan hajji da umrah a  kasar Saudiyya ta fitar da sanarwa, inda a cikin take bayani kan kayyade adadinin mutanen da za su iya samun damar sauke farali a shekarar, inda bayanin ya ce mutane dubu 60 kawai za a yarje wa sauke farali.

Bayanin ya ce daukar wanann matakin ya zo ne sakamakon sake bullar wasu sabbin nau’oin cutar corona a kasashen duniya daban-daban, wanda hakan yasa ala tilas a dauki matakai na kayyade adadin mutanen da za su taru a wuri guda domin gudanar da ayyukan ibada na hajji ko umra, domin ba su kulawar da ta kamata a bangaren kiwon lafiya.

Haka nan kuma bayanin ma’aikatar kula da ayyukan hajji da umrah ta  kasar Saudiyya ya yi ishara da cewa, dukkanin adadin muaten dole ne su kasance a cikin kasar ta Saudiyya, ‘yan kasa ne ko ‘yan kasashen ketare, sannan kuma shekarunsu ya zama tsakanin 18 zuwa 65.

 

3976995

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* :