IQNA

Jagoran Juyi Na Iran: Salon Siyasar Kasashen Yammacin Turai Na Kunshe Da Munafunci Da Yaudara

18:34 - June 28, 2021
Lambar Labari: 3486056
Tehran (IQNA) Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa har kullum kasashen yammacin duniya suna bin salon siyasar munafunci da harshen damo ne.

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya caccaki wasu ƙasashen yammaci saboda irin goyon bayan da suke ba wa ‘yan ta’adda a daidai lokacin da suke ci gaba da ikirarin kare haƙƙoƙin bil’adama.

Jagoran ya bayyana hakan ne a yayin wata ganawa da yayi a yau Litinin da shugaba da jami’an ɓangaren shari’a na Jamhuriyar Musulunci ta Iran inda yayin da ya ke magana irin yadda mambobin ƙungiyar munafukai ta MKO masu adawa da gwamnatin Musulunci ta Iran suna ci gaba da walwalarsu a ƙasar Faransa da sauran ƙasashen Turai ba tare da wata tsangwama ba ya bayyana cewar:

Gwamnatin Faransa da sauransu ba tare da jin kunya ba suna magana kan kare haƙƙoƙin bil’adama a daidai lokacin da suke ci gaba da ɗaukar baƙuncin waɗannan makasa, suke goyon bayansu, har ma suke ba su waje a majalisun ƙasashensu.

Yayin da yake magana kan kisan gillan da ‘yan ƙungiyar MKO ɗin suka yi wa tsohon alkalin alƙalan ƙasar ta Iran Ayatollah Mohammad Beheshti da mataimakansa a ranar 28 Yunin 1981 kuwa, Ayatollah Khamenei ya ce: MKO ɗin sun aikata munanan aika-aika kan al’ummar Iran ta hanyar kisan gillan da suka yi wa wannan Ayatullah Beheshtin da wasu mutane 70 a wannan rana shekaru arba’in ɗin da suka gabata.

A wani ɓangare na jawabin nasa, Ayatollah Khamenei ya sake jinjinawa al’ummar Iran saboda fitowar da suka yi yayin zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar a ranar 18 ga watan Yunin nan, yana mai cewa duk da ƙoƙarin da maƙiya suka yi wajen dushe hasken zaɓen amma wannan ƙoƙari na su ya zama aikin baban giwa.

Alƙalin alƙalai kuma shugaban ɓangaren shari’a na Iran ɗin Sayyid Ibrahim Ra’isi da ‘yan tawagarsa ta manyan jami’an ɓangaren shari’ar sun kai wa Jagoran ziyara ne yau ɗin a daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan makon ma’aikatar shari’a ta ƙasa a Iran ɗin don tunawa da kisan gillan da ‘yan ƙungiyar munafukai ta MKO suka yi wa tsohon alkalin alƙalan ƙasar ta Iran Ayatollah Mohammad Beheshti da mataimakansa su saba'in da biyu a farko-farkon nasarar juyin juya halin Musulunci a ƙasar.

 

3980545

 

 

captcha