A rahoton da jaridar Quds Al-arabi ta bayar, kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Falasɗinu, Hamas, da ma’aikatar harkokin wajen gwamnatin cin gashin kan Falasɗinawan sun yi Allah wadai da kalaman shugaban ƙasar Jamus Frank-Walter Steinmeier na cewa kotun duniya mai shari’ar manyan laifuffuka ICC ba ta da hurumin binciken laifukan yaƙin da Isra’ila ta aikata kan Falasɗinawa.
A wata sanarwa da ta fitar ɗauke da sanya hannun kakakinta, Hazem Qassem, ƙungiyar Hamas ɗin ta bayyana cewar kalaman shugaban Jamus na rashin hurumin kotun ICC ɗin na binciken aika-aikan Isra’ila kan al’ummar Falasɗinu yin karen tsaye ne ga dokokin ƙasa da ƙasa da kuma ci gaba da goyon bayan Isra’ilan ido rufe.
Sanarwar ta ƙara da cewa kalaman shugaban na Jamus tamkar kwaɗaitar da Isra’ila ɗin ne ta ci gaba da ɗanyen aikin da take yi da kuma sanya ta a matsayin wacce take sama da dokokin duniya.
Ita ma a nata ɓangaren Ma’aikatar harkokin wajen Falasɗinun ta yi tir da kalaman shugaban na Jamus tana mai bayyana ta a matsayin karen tsaye ga dokokin ƙasa da ƙasa da kuma tsoma baki cikin ayyukan ICC.
Don haka sai Ma’aikatar ta buƙaci shugaban da kuma gwamnatin Jamus da su daina goyon bayan ɓangare guda da suke yi wanda hakan ya ba wa Isra;ilan kariya da kuma ɗora ta sama da dokokin ƙasa da ƙasa.
Shugaban na Jamus dai yayi wannan kalamin ne cikin wata tattaunawa da yayi da jarifar Haaretz ta Isra’ilan inda ya ce yana tsananin adawa da shirin kotun ICC ɗin na ƙaddamar da bincike kan aika-aikan Isra’ilan kan Falasɗinawa yana mai cewa kotun ba ta da hurumi kan gwamnatin Isra’ila.
A watannin baya ne dai, tsohuwar mai shigar da ƙara kotun ta ICC Malama Fati Bensouda ta sanar da shirin fara gudanar da bincike kan aika-aikan da aka tafka a yankunan Falasɗinawa waɗanda suke ƙarƙashin mamayar Isra’ila.