IQNA

Masallacin Sulaimaniyya Daya Daga Cikin Muhimman Wuraren Tarihin Musulunci A Turkiyya

23:21 - July 03, 2021
Lambar Labari: 3486073
Tehran (IQNA) masallacin Sulaimaniyya na daya daga cikin muhimman wuraren tarihin musulunci a kasar Turkiyya.

Bisa rahoton kamfanin dillancin labaran iqna, masallacin Sulaimaniyya wanda aka gina shi bisa umarnin sarki Sultan Sulaiman Qanuni, daya daga cikin sarakunan daular Usmaniyya, yana daya daga cikin muhimman wuraren tarihin musulunci da ke birnin Istanbul a kasar Turkiyya a halin yanzu.

Wani kwararren magini musulmi mai suna Sinan ne ya gina wannan masallaci, an kuma bude masallacin nea  ranar 5 ga watan Oktoban shekara ta 1557 miladiyya.

Masanin tarihi Ibrahim Bachawi ya bayyana cewa, an yi amfani da kudin zinari da ya kai kilogram 3200 wajen aikin ginin wannan masallaci, sannan kuma ma'aikata 523 ne suka yi aikin ginin.

A cikin wanann masallaci akwai babban dakin karatu da aka gina, wanda ya kunshi littafai na addini da yawansu ya kai tsakanin dubu 90 zuwa dubu 120, kimanin kashi 60 zuwa 70 cikin dari na littafan an rubuta a cikin harshen larabci ne.

Sai kuma kimanin kashi 25 zuwa 30 an rubuta sua  cikin harshen Turkanci ne, sai kashi 12 zuwa 15 an rubuta a cikin harsunan Farisanci da kuma wasu harsuna na daban.

3979566

 

captcha