Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, kamfanin salam sisters kamfani ne da yake samar da kayayyakin wasan yara ta hanyar da za ta taimaka wajen tarbiyarsu bisa tsari na addinin musulunci.
Wannan kamfani yana gudanar da ayyukansa ne bisa tsari, ta yadda yake samar da kayayyakin wasa na yara wadanda ba za su kawar da hankalinsu daga koyarwa addini ba, da hakan ya hada da samar 'yar bebi amma da lullubi irin na addini, babu nuna tsiraici.
Haka nan kuma sauran kayan wasa da suka hada da wasanni na kwamfuta, duk suna bisa tsari ne wanda ba zai kautar da yara daga turbar addini ba.
Kayan da kamfanin yake samarwa musamman na wasannin ga kananan yara na samun karbuwa ga iyalai usulmi musamman wadanda suke zaune a kasashen turai, da kuma kasashen da ba na musulmi ba.
Baya ga kayan wasa, akwai wasu kayan wadanda kamfanin ya samar wadanda su kuma na koyar da yara ne, da suka hada da na'urorin kwamfuta na yara, wadanda aka sanya musu wata manhaja ta musamman.
Daga cikin irin abubuwan da ake saka wa wannan manhaja har da koyar da karatun kur'ani mai tsarki ga yara, da kuma haruffan larabci ta hanya mai sauki.