IQNA

Macron Ya Ce Faransa Za Ta Kwashe Sojojinta Daga Mali Nan Da Watanni

17:12 - July 14, 2021
Lambar Labari: 3486104
Tehran (IQNA) Faransa tana shirin kwashe sojojinta daga kasar Mali nan da wasu watanni masu zuwa.

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, a cikin wani jawabinsa da ya gabatar a yau a lokacin da karbi faretin sojoji na ranar kasa, ya bayyana cewa, Faransa tana da shirin kammala kwashe sojojinta daga kasar Mali a cikin watanni uku na farkon shekara mai zuwa.

Ya ce; kasantuwar sojojin Faransa a cikin Mali da yankin Sahel ne ya hana kafa gwamnatin Daesh a yankin, wanda a cewarsa hakan babbar nasara ce ga Faransa, kuma sun cimma burinsu na zuwa Mali domin dakushe kaifin kungiyoyin 'yan ta'adda.

A zaman da ya halarta tare da shugabannin kasashe biyar na yankin Sahel a ranar Juma’a da ta gabata, Macron ya sheda cewa; Faransa za ta fara janye dakarunta daga yankin sahel daga nan zuwa karshen wannan shekara da muke ciki, kamar yadda kuma za ta rufe sansanonin sojin nata da ke arewacin kasar Mali kafin karshen wannan shekara.

Tun a ranar daya ga watan Aguskatn shekara ta 2014 ne dai Faransa ta jibge sojojinta a cikin kasar Mali da sunan yaki da kungiyoyin ‘yan ta’adda masu da’awar jihadi.

Kasar Mali dai tana daga cikin kasashen yammacin nahiyar Afirka da suke fama da matsaloli da suke da alaka da kungiyoyin ‘yan ta’adda da suke kai aki hare-hare da sunan addini.

 

 

3984101

 

 

captcha