IQNA

Mahajjata Suna Gudanar Da Aikin Hajji A Cikin Kwararan Matakai Na Kiwon Lafiya

Tehran (IQNA) Shekara ta biyu kenan a jere da ake gudanar da aikin hajji a cikin yanayi na corona.

Shekara ta biyu kenan a jere da ake gudanar da aikin hajji a cikin yanayi na corona, inda hukumomin Saudiyya suka kayyade cewa mutane dubu 60 ne kawai za su gudanar da aikin hajjin bana saboda kaucewa yaduwar cutar corona, baya ga haka kuma dole ne mahajjatan su cika sharuddan da aka gindaya musu na yin allurar rigakafin cutar corona, da kuma kasancewa a cikin kasar ta Saudiyya a lokacin fara rijistar daukar maniyyaya.