IQNA

21:24 - July 29, 2021
Lambar Labari: 3486150
Tehran (IQNA) A cikin bayanin Harkar musulinci a Najeriya ta bayyana hukuncin sakin Sheikh El-Zakzaky da mai dakinsa a matsayin babbar nasara.

Wannan ya zo ne a cikin wata sanarwa da shugaban dandalin yada labarai na Harka Islamiyya Ibrahim Musa ya aike wa manema labarai, ta ce hukuncin ya wanke dukkan magoya bayan Harka Islamiyyaa Najeriya.

Ranar jiya Laraba ne Babbar kotun jihar Kaduna ta bayar da umarnin a saki Sheikh Ibrahim El-Zakzaky tare da matarsa Zeenat, inda ta wanke su daga dukkan zargin da ake yi a kansu wanda akansa ne a  aka tsare su tsawon shekaru kusan shida.

Wannan hukunci na kotu dai ya wanke Sheikh Ibrahim Zakzaky da maidakinsa daga dukkanin tuhumce-tuhumcen da ake yi musu, wanda gwamnatin Jihar Kaduna ta gabatar ga kotun, kuma an salli shari'ar ne saboda babu wasu hujjoji da suke tabbatar da abin da ake zarginsu.

 

3987241

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: