Kamfanin dillancin labaran sputnik ya bayar da rahoton cewa, Irim Ashkin yarinya ce 'yar shekaru 15 daga garin Quniya na kasar Turkiya wadda ta hardace kur'ani a cikin kwanaki casa'in da uku.
Malamar da da take koyar da wannan yarinya wajen hardar kur'ani ta bayyana cewa, da farko dai ta fara ne da hardar shafi 1 zuwa 5, amma daga bisani ta mayar da tsarin nata zuwa hardar shafuka 15 a kowace rana.
Ta ce da farko dai tana a wani aji ne na harda, to amma saboda la'akari da cewa tana saurin hardace duk abin da ta karanta, wannan ya sanya an kai zuwa wani aji na daban.
Duk da haka yadda take yin hardar a cikin sauri ya zama abin mamaki ga kowa domin kuwa tana yin hardar ne fiye da abin da ake koyar da ita, saboda baiwar da Allah ya yi mata, inda a cikin kwana casa'in da uku ta kammala hardar kur'ani baki dayansa.