IQNA

Shugaban Kasar Afghanistan Ya Fice Daga Kasar Bayan Da Taliban Ta Kwace Iko Da Kabul A Yau

21:17 - August 15, 2021
Lambar Labari: 3486206
Tehran (IQNA) shugaban kasar Afghanistan ya bar kasar zuwa kasar Tajikistan bayan da mayakan Taliban suka birnin Kabul a yau.

shugaban ƙasar Ashraf Ghani ya fice daga ƙasar inda wasu rahotannin suka ce ya tafi ƙasar Tajikistan, hakan kuwa yana zuwa ne a daidai lokacin da mayaƙan ƙungiyar Taliban suka yi wa birnin Kabul, babban birnin Afghanistan ɗin ƙawanya.

Har ya zuwa yanzu dai babu wani cikakken bayani dangane da abin da ya sanya shugaba Ghanin ya bar ƙasar, to sai dai rahotanni suna nuni da cewa ɗaya daga cikin buƙatun ƙungiyar ta Taliban shi ne shugaban ya bar mulki, don kuwa suna ganinsa a matsayin wanda ya ke ƙafar ungulu ga shirin tattaunawar sulhu da ake yi a ƙasar.

A ɓangare guda kuma kakakin ƙungiyar ta Taliban Suhail Shaheen ya ce suna fatan ganin an miƙa mulki cikin ruwan sanyi cikin ‘yan kwanaki masu zuwa, yana mai cewa ƙungiyar za ta kare haƙƙoƙin al’ummar Afghanistan ɗin ciki kuwa har da haƙƙoƙin mata, yana mai cewa ƙungiyar a shirye take ta bar duk wani wanda ya ke son barin birnin na Kabul da suka yi masa ƙawanya.

Wasu rahotannin dai suna nuni da cewa ɓangarori daban-daban na ‘yan siyasa da manyan jami’an gwamnatin ƙasar ta Afghanistan suna ci gaba da tattaunawa kan yadda za a magance rikicin da ya kunno kai a ƙasar, inda aka ce a gobe za a ci gaba da tattauanwar da ake yi tsakanin gwamnatin Afghanistan ɗin da tawagar ‘yan Taliban ɗin a birnin Doha na ƙasar Кatar.

A yau da rana tsaka ne dai ma’aikatar harkokin cikin gida a kasar Afghanistan ta sanar da cewa, mayakan Taliban sun fara shiga birnin Kabul ne a yau ta dukkanin bangarorin birnin.

Sannan kuma bayanin ya ce, bayan shiga birnin sun mamaye jami’ar Kabul da ke yammacin birnin, inda suka kafa tutocinsu a kan gine-ginen jami’ar, sannan kuma yanzu haka suna ci gaba da kara nausawa zuwa wasu sassan birnin.

Da jijjifin safiyar yau ne dai aka fara kwashe kayayyaki daga ma’aikatun gwamnati, kamar yadda kuma jami’ai da dama suka fice daga birnin.

3990988

 

 

 

captcha