Tun daga farkon watan Muharram kamfanin dillancin labaran iqna yana kokarin kawo bayanai daga masana daga sassan duniya da suka yi kan lamarin da ya shafi waki'ar Ashura da kuma sadaukarwar da Imam Hussain (AS) da sahabbans da kuma iyalan gidan manzon Allah (SAW) suka yi a wannan rana.
Edward Kessler fitaccen masani ne kan ilimin falsafama a kasar Burtaniya kuma daya daga cikin manyan malamai na jami'ar Cambriedge, wanda ya yi tsokaci kan sadaukarwar Imam Hussain (AS) a ranar ashura.
A cikin bayanin nasa ya bayyana wannan babbar sadaukarwa da cewa, tana a matsayin abin da ke koyar da yin tsayin daka wajen tabbatar adalci a cikin rayuwar 'yan adam ta zamantakewa, da kuma bayar da kariya ga lamari na gaskiya.
Za a iya kallon hoton bidiyo na bayanin nasa a nan: