IQNA

Sayyid Nasrullah Ya Yi Jan Kunne Ga Amurka Da Isra'ila Da Babbar Murya

17:39 - August 19, 2021
Lambar Labari: 3486218
Tehran (IQNA) Sayyid Hassan Nasrullah ya gargadi Amurka da Isra’ila da kawayensu kan taba jrgin ruwan da ke dauke da mai daga Iran zuwa Lebanon.

Babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrullah ya gargadi Amurka da Isra’ila da kawayensu, da kada su yi gigin taba jrgin ruwan da ke dauke da mai daga Iran zuwa Lebanon.

Sayyid Nasrullah ya bayyana hakan ne yau a cikin bayaninsa na ranar Ashura, inda ya sheda cewa, ‘yan sa’oi kadan suka rage katafaren jirgin ruwan Iran dauke da man fetur ya iso gabar ruwan birnin Beirut na kasar Lebanon.

Ya ce wannan hakki ne na gwamnatin kasar Lebanon da ya rataya a kanta da ta samar da wadataccen mai ga dukkanin al’ummar kasar Lebanon, amma saboda matsalolin da aka jefa kasar hakan ya gagara, wanda hakan ne kuma yasa ala tilas Hizbullah ta shiga cikin lamarin domin saar da wadataccen mai ga al’ummar kasar Lebanon daga kasar Iran.

Ya kara da cewa baya ga wannan jirgin, akwai wasu suna nan tafe dauke da man fetur da dangoginsa, wada kuma hakan yana lamari ne da ya shafi rayuwar al’ummar kasar Lebanon, saboda haka ya ce yana gargadin Amurka da Isra’ila da sauran kawayensu da su kiyaye, domin taba wadannan jiragen man yana a matsayin taba al’ummar Lebanon ne baki daya, wanda Hizbullah a shirye take ta yi komai a kan hakan.

Sannan kuma ya yi ishara da cewa, bayan kashin da Amurka ta sha a Afghanistan da ficewar da ta yi daga kasar a cikin kaskanci da kunya, a halin yanzu hankula sun koma kan Amurka a cikin kasashen Syria da Iraki, wanda a can ma za ta fice a cikin kaskanci da kunya.

 

3991734

 

 

 

captcha