IQNA

Katafaren Jirgin Ruwan Mai Na Iran Na Gab Da Isa Kasar Lebanon

17:35 - September 04, 2021
Lambar Labari: 3486268
Tehran (IQNA) mutanen Lebanon na jiran isowar katafaren jirgin ruwan Iran daukle da makamaashi domin taimaka kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a yau Asabar daruruwan mutane sun taru a kusa da tashar jiragen ruwa ta birnin Beirut, domin nuna farin cikinsu da shirin Iran na aike wa da katafaren jirgin ruwa da yake dauke da makamashi zuwa kasar ta Lebanon.

Rahoton ya ce wannan na zuwa ne a daidai lokacin da jirgin na Iran wanda yake dauke da makamashi yake kan hanyarsa ta isa gabar ruwan Beirut, bayan da ya yada zango a gabar ruwan kasar Syria.

Kasar Lebanon dai ta shiga cikin matsanancin hali sakamakon rashin makamshi, bayan da Amurka da wasu kasashen turai suka dauki matakin takurawa kasar, da nufin ganin sun raunana kungiyar Hizbullah, wadda suke kallonta  a matsayin babbar barazana ga gwamnatin yahudawan Isra’ila.

 

3995015

 

captcha