IQNA

'Yan Sanda Sun Kame Wata Mata Mai Tsafi Tare Da Wulakanta Ayoyin Kur'ani A Aljeriya

16:59 - September 13, 2021
Lambar Labari: 3486302
Tehran (IQNA) 'yan sanda a kasar Aljeriya sun kame wata matsafiya mai wulakanta ayoyin kur'ani mai tsarki a kasar Aljeriya.

Tashar alkhabar ta bayar da rahoton cewa, 'yan sanda a kasar Aljeriya sun kame wata matsafiya mai wulakanta ayoyin kur'ani mai tsarki a jihar Tipasa a kasar Aljeriya.

Bayanin jami'an tsaron ya ce, an samu wasu kayan saddabaru da surkulle da sakandamomi a gidan matar, wadda take yaudarar mutane da yi musu rufa ido da sunan yi musu magani, ta hanyar magana da aljannu da dai sauran hanyoyi an yaudara.

Baya ga haka kuma an samu ayoyin kur'ani a cikin kayan surkullen nata, wanda aka hada su da wasu karikitai marassa kan gado, wanda hakan yake a matsayin wulakanta ayoyin kur'ani mai tsarki, kuma hakan babban laifi ne a cikin dokokin kasar Aljeriya.

Yanzu haka dai an yi awon gaba da matar da kuma wasu daga cikin masu wurinta da sunan neman magani.

3997172

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: surkulle ، yaudara ، sakandamomi ، saddabaru ، matsafiya
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha