IQNA

Amurka Ce Ta Bayar Da Dama Ga Taliban Har Ta Kwaci Mulki A Afghanistan

20:09 - September 14, 2021
Lambar Labari: 3486310
Tehran (IQNA) kwararra kan harkokin siyasar yankin gabas ta tsakiya a jami'ar Washington ta bayyana kwatar mulkin da Taliban ta yi a Afghanistan da cewa shirin Amurka ne.

A zanatawar da ta hada ta da kamfanin dillancin labaran Iqna, kwararra kan harkokin siyasar yankin gabas ta tsakiya a jami'ar Washington Farfesa Shanthie Mariet D’Souza ta bayyana kwatar mulkin da Taliban ta yi a Afghanistan da cewa shirin Amurka babu tantama.

Shanthie Mariet D’Souza ta ci gaba da cewa, tun daga lokacin da Amurka ta shiga tattaunawa da Taliban a Qatar, alamun hakan suka fara bayyana a fili, domin kuwa Amurka tana da masaniya a kan dukkanin halin da Taliban take ciki da kuma shirinta na kwace mulkin kasar Afghanistana  duk lokacin da ta samu damar yin hakan.

Sannan kuma a cewar Shanthie Mariet D’Souza, babu wani abin da ya canja dangane da kungiyar Taliban na tsattsauran ra'ayi, dukkanin abin da take fadi na canji a  cikin lamurranta wawantar da al'ummomin duniya ne kawai take yi.

Ta ce daga lokacin da Taliban ta kwace mulki a kasar Afghanistan 'yan makonni da suka gabata, ya zuwa yanzu an ga  'yan Taliban a wurare da dama suna zartar da hukuncin kisa a kan mutane bisa abin da suke kira saba wa shari'ar musulunci a  mahangarsu.

Haka nan kuma an ga suna zane mutane da bulala a matsayin hukunci a kan wadanda ba su tsayar da gemo ko dage wando ba, ko kuma mata wadanda lullubinsu bai rufe kansu ba sosai, da dai sauran matakai na tsatsauran ra'ayi da aka san Taliban da su a baya  a cewarta, lamarin da ta ce hakan ishara ce ta cewa za a koma 'yar gidan jiya a kasar Afghanistan, kuma Amurka ita ce ummul haba'isin hakan.

 

3993918

 

Abubuwan Da Ya Shafa: makonni da suka gabata ، Taliban ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha