IQNA

An Rufe Dukkanin Ma'aikatun Gwamnati A Karbala Domin Tarukan Arba'in

18:19 - September 23, 2021
Lambar Labari: 3486342
Tehran (IQNA) mahukunta a kasar Iraki sun sanar da rufe dukkanin ma'aikatu a birnin Karbala domin shirin gudanar da tarukan arba'in.

Kamfanin dillancin labaran kasar Iraki ya bayar da rahoton cewa, gwamnan lardin Karbala Nasif Jasem Alkhitabi ya sanar da cewa, daga yau Alhamis an rufe dukkanin ma'aikatun gwamnati a birnin Karbala, domin shirin gudanar da tarukan ziyarar arba'in na Imam Hussain (AS).

Ya ci gaba da cewa, kamar yadda aka saba a kowace shekara ana dakatar da dukkanin ayyuka a ma'aikatun gwamnatia  lokacin tarukan arba'in, domin bayar da dama ga tsare-tsare na wannan taruka,a  kan haka a wannan karon ma daga yau an rufe dukkanin ma;aikatun gwamnati a lardin na Karbala da ke kudancin Iraki.

Baya ga bangaren ayyukan gwamnati, an dakatar da ayyuka daban-daban wadanda ba su shafi bangaren kiwon lafiya da tsaro da kuma harkokin kasuwancin mutane ba.

A nasu bangaren dakarun sa kai na hashd Shaabi suna cikin masu taimaka ma jami'an tsaro wajen gudanar da ayyukansu, kamar yadda kuam suke taimaka wa bangaren ayyukan lafiya da bayar da agajin gaggawa.

 

3999606

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa:
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha