IQNA

An Raya Ranakun Ziyarar Arbaeen A Wasu Yankuna A Najeriya

16:17 - September 28, 2021
Lambar Labari: 3486360
Tehran (IQNA) an raya ranakun ziyarar Arbaeen a wasu yankuna na Najeriya a jiya.

Tashar PressTV ta bayar da rahoton cewa, an raya ranakun ziyarar Arbaeen a wasu yankuna na Najeriya a jiya.

A wasu shekaru a baya magoya bayan Harka Islamiyya sun fara gudanar da tattaki a daidai irin wannan lokaci daga yankuna daban-daban zuwa Zaria.

Bayan dakatar da tattakin na tsawon wasu shekaru biyo bayan kisan gillar Zaria, sun dakatar da gudanar da wanann tattaki, amma shekarar bana wasu daga cikin magoya bayan Harka Islamiyya sun yi irin wannan tattaki a wannan lokaci na ziyarar arbaeen.

Baya ga haka kuma a wasu bangarorin an gudanar ad taruka ne tare da yin jawabai kan wannan rana da kuma abubuwan da suka faru tun ranar Ashura har zuwa cikar kwanaki arba'in bayan shahadar Imam Hussain (AS). 

 

 

 

 

 

برگزاری راهپیمایی اربعین با حضور هزاران نفر از شیعیان در نیجریه

برگزاری راهپیمایی اربعین با حضور هزاران نفر از شیعیان در نیجریه

Abubuwan Da Ya Shafa: tarukan arbaeen ، Najeriya ، wasu yankuna
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha