IQNA

Jagoran Kiristocin Birnin Quds Ya Ce Ba Za Su Amince da keta Alfarmar Masallacin Quds Ba

16:35 - October 03, 2021
Lambar Labari: 3486378
Tehran (IQNA) shugaban kiristocin Quds ya bayyana cewa, ba za su taba amincewa da keta alfarmar masallacin Quds da yahudawan Isra'ila suke yi ba.

 Shafin yada labarai na Alwifaq news ya bayar da rahoton cewa, Atallah Hanna shugaban kiristocin birnin Quds ya bayyana cewa, ba za su taba amincewa da keta alfarmar masallacin Quds da yahudawan Isra'ila suke yi ba.

Atallah Hanna ya bayyana take-taken gwamnatin yahudawan Isra'ila da take dauka na keta alfarmar masallacin Quds da cewa, hakan yana a matsayin keta alfarmar dukkanin adinai ne na ubangiji da aka saukar daga sama, ba addinin muslucni kawai ba.

saboda haka ya ce kiristoci da musulmi da ma yahudawa masu lamiri gami da sauran al'ummomin duniya masu kishin 'yan adamtaka a sahu guda domin kalubalantar wannan mataki na yahudawan sahyoniya.

Atallah Hanna dai yana daga cikin jagororin mabiya addinin kirista wadanda suke yin sadaukarwa wajen al'ummar falastinu da wurare masu tsarki na muuslmi da kirista da suke a birnin Quds.

Koa  lokacin yakin da Isra'ila ta kaddamara  'yan watannin da suka gabata, ya yi ta shirya taruka da jerin gwano domin nuna goyon baya ga al'ummar yankin zirin zirin Gaza, tare da la'antar zaluncin Isra'ila a kansu.

 

4001929

 

captcha