IQNA

Jami'an Tsaron Isra'ila Sun Kai Hari Kan Gidan Babban Limamin Masallacin Quds

18:57 - October 10, 2021
Lambar Labari: 3486410
Tehran (IQNA) jami'an tsaron Isra'ila sun kai hari kan gidan Sheikh Ikrama Sabri babban limamin masallacin Quds.

Tashar Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, da jijjifin safiyar yau L:ahadi ne jami'an tsaron Isra'ila suka kai hari kan gidan Sheikh Ikrama Sabri babban limamin masallacin Quds, sannan kuma suka kama suka tafi da shi.

Jami'an tsaron yahudawan sun tsare Sheikh Ikrama na wani lokaci a ofishin 'yan sanda da ke yankin Maskubiyya a yammacin birnin Quds, ba tare da wani dalili ba.

Bayan kwashe wani lokaci suna ta yi masa tambayoyi, daga baya sun bukaci da ya sanya hannu a kan wata takarda, wadda ta kunshi bayanin cewa za a tayar da shi daga birnin Quds baki daya, tare da mayar da shi wani yanki na daban a cikin Falastinu domin ya ci gaba da rayuwa a can tare da iyalansa.

Sheikh Ikramah yaki amincewa ya sa hannu a kan takardar, duk kuwa da cewa jami'an tsaron yahudawan sun dage a kan haka, amma daga karshe sun sake shi ba tare da yasa hannu a kan takardar ba.

bayan dawowa gidansa, tashar Aljazeera ta zanta da shi, inda ya sheda cewa, manufar yahudawan ita ce tilasta ya yi shiru da bakinsa a kan zaluncin da suke yi wa al'ummar Falastinu ko kuma su kore shi daga garinsa na haihuwa wato birnin Quds, inda ya tabbatar musu da cewa ba zai shiru ba, kuma ba zai bar garinsa ba.

 

4003604

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa:
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha