IQNA

Yara Mahardata Kur'ani Na Gudanar Da Zagaye A Garin Gaza Na Falastinu A Kowace Shekara

18:18 - October 11, 2021
Lambar Labari: 3486412
Tehran (IQNA) kamar kowace yara mahardata kur'ani mai tsarki a garin Gaza na Falastinu suna gudanar da wani zagaye a kowace shekara.

Shafin yanar gizo na tashar Aljazeera ya bayar da rahoton cewa, kamar kowace yara mahardata kur'ani mai tsarki a garin Gaza na Falastinu suna gudanar da wani zagaye a kowace shekara.

Makarantun da suke koyar da yaran ne suke shirya wannan zagaye a kan titunan birnin Gaza, da nufin kara tabbatar wa duniya cewa, duk da irin mawuyacin halin da suke ciki na killacewa da fuskantar hare-haren yahudawa, amma sunan nan a kan bakansu an riko da addini da kuma koyarwar kur'ani mai tsarki.

Jamal Hindi shugaban kwamitin gudanarwa na kungiyar Hamasa  yankin zirin Gaza ya bayyana cewa, makarantu suna iyakacin kokarinsu wajen koyar da yara dukkanin ilmomia  makarantu a zirin Gaza, da hakan ya hada da makarantun addini.

Akwai dubban yara da suka hardace kur'ani a yankin Zirin Gaza wadanda suke samun tarbiya a makarantun kur'ani da suke yankin.

راهپیمایی «اهل قرآن» در خیابان‌های غزه + عکس

راهپیمایی «اهل قرآن» در خیابان‌های غزه + عکس

 

4003856

 

 

captcha