IQNA

Iran Ta Aike Da Jirgi Dauke Da Taimako Zuwa Afghanistan

22:13 - October 11, 2021
Lambar Labari: 3486414
Tehran (IQNA) Iran ta aike da taimako zuwa ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu da kuma wadanda suka jikkata a harin da aka kai a masallaci a gundumar Kunduz da ke Afghanistan.

Ofishin jakadancin Iran da ke birnin Kabul na kasar Afghanistan ya sanar da cewa, a yau gwamnatin Iran ta aike da taimako zuwa ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu da kuma wadanda suka jikkata a harin da aka kai a masallaci a gundumar Kunduz, inda mutane da dari suka rasa rayukansu wasu fiye da dari biyu kuma suka jikkata.

An dai kai harin ta'addanci ne a ranar Juma'a a kan wani masallaci a Lardin Kunduz a lokacin da ake sallar Juma'a, kuma rahotanni sun tabbatar da cewa, wani dan ta'adda ne da ya yi jigidar bama-bamai ya tarwatsa kansa a tsakiyar masallata a lokacin sallar Juma'a a masallacin mabiya mazhabar Ahlul bait a yankin Khan Abad da ke cikin gudumar ta Kunduz.

Mai magana da yawun kungiyar Taliban Zabihullah Mujahid ya fitar da bayani da ke yin tir da Allawadai da harin, tare da shan alwashin cewa wadanda suka kai harin za su dandana kudarsu, domin kuwa za su fuskanci hukunci mai tsanani.

Kungiyar 'yan ta'addan Daesh ta fitar da sanarwa da ke cewa, ita ce take da hannu a wannan harin kamar dai yadda aka zata tun daga farko.

Majalisar Dinkin Duniya gami da kungiyar kasashen musulmi da cibiyar Azhar ta Masar, da kuma cibiyoyin ilimi na Iran da Iraki da gwamnatocin kasashe da dama a duniya duk sun yi tir da Allawadai da harin.

 

4003943

 

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha