IQNA

Isra’ila Ta Fara Rusa Babbar Makabartar Tarihi Ta Musulmi A Birnin Quds

16:47 - October 19, 2021
Lambar Labari: 3486445
Tehran (IQNA) wata kotun Isra’ila ta bayar da umarnin rusa wata makabartar musulmi a yankin Yusufiyya da birnin Quds.

Kamfanin dillancin labaran Safa ya bayar da rahoton cewa, wata kotun Isra’ila ta bayar da umarnin rusa wata makabartar musulmi a yankin Yusufiyya da birnin Quds.

Tun makon da ya gabata ma’aikatar magajin gari a birnin Quds da ke karkashin mmayar yahudawa, ta bayar da umarnin fara rusa wannan makabarta mai tsohon tarihi a musulunci, inda yahudawa suke yin amfani da motocin budoza wajen rusa makabartar.

Rahotanni sun ce yahudawan suna rusa kabrukan msuulmi, inda suke tune gawarwakin da ke wuri da wasunsu sun zama kasusuwa, amma duk da haka suna nike su da kasar wurin.

Daya daga cikin falastinawa amsu kula da makabartun musulmi a birnin Quds Mustafa Abu Zahra ya bayyana cewa, dama tuni sun yi zaton hakan za ta faru, bisa la’akari da take-taken gwamnatin yahudawan Isra’ila.

Makabartar Yusufiyay dai tana da tsohon tarihi a cikin addinin muslunci, amma gwamnatin yahudawan Isra’ila ta ce ginin makabartar ya sabawa ka’ida ta tsarin gine-gine a birnin Quds.

 

4006152

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha