IQNA

An Kaddamar Da Littafin Mausu'a Na Marigayi Ayatollah Taskhiri A Taron Makon Hadin Kan Musulmi

20:05 - October 19, 2021
Lambar Labari: 3486448
Tehran (IQNA) a yayin bude taron kasa da kasa na makon hadin kan musulmi a birnin Tehran na kasar Iran a yau an kaddamar da littafin Mausu'a na marigayi Ayatollah Taskhiri.

A lokacin bude taron kasa da kasa na makon hadin kan musulmi a birnin Tehran na kasar Iran a yau Talata, an kaddamar da littafin Mausu'a na marigayi Ayatollah Muhammad Ali Taskhiri, tare da halartar shugaban kasar Iran Ibrahim Ra'isi.

Baya ga shugaban na Iran wasu daga cikin malamai da suka hada da babban sakataren cibiyar kusanto da mazhabobin musulunci ta duniya Sheikh Hadid Shahriyari, sun halarci wurin.

Littafin na Mausu'a wanda marigayi Ayatollah Sheikh Muhammad Ali Taskhiri ya rubuta a cikin mujalladai 12, ya kunshi bangarori daban-daban na ilmomin addini.

4006338

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha