IQNA

Wasu 'Yan Majalisar Amurka Sun Buka A Bude Ofishin Yaki Da Akidar Kyamar Musulmi

22:43 - October 22, 2021
Lambar Labari: 3486460
Tehran (IQNA) Ilhan Omar 'yar majalisar dokokin Amurka ta bukaci a kafa wani ofishi da zai yaki kyamar musulunci.

Tashar Fox 9 ta bayar da rahoton cewa, Ilhan Omar 'yar majalisar dokokin Amurka daga jam'iyyar Democrat tare da Jan Schakowsky ita ma daga jam'iyyar Democrat sun bukaci a kafa wani ofishi da zai yaki kyamar musulunci.

Aikin wannan ofishi dai shi ne sa ido, da kuma yakar ayyukan kyamar musulunci da musulmi da tsokana, wanda za a bude a kasashe daban-daban domin hakan.
 
A cewar Ilhan Omar, ofishin yin zai taimaka wa masu tsara manufofin siyasar Amurka, su kara fahimtar matsalar musulmi a duniya da kuma yadda ake nuna kyama ga gare su saboda addininsu.
 
Ta ce, "A Minnesota, masu yin zagon ƙasa suna aika saƙon ƙiyayya ga musulmi mai dauke da alamar sakandamin Nazi," in ji ta.
 
Haka nan kuma ta yi magana game da cin zarafin da ake yi wa 'yan kabilar Uighur a China,da 'yan Rohingya a Burma, da kuma cin zarafin Musulmai a Indiya da Sri Lanka. 
 
Ta kara da cewa, “Ire -iren wadannan abubuwa sun zama ruwan dare ga Musulmai a Amurka da kasashen waje da hakan ya hada da wasu kasashen turai.
 
Ta ce, a matsayinmu na sadaukar da kai wajen kare 'yancin addini na duniya da' yancin ɗan adam, dole ne mu gane cewa kyamar Islama da ake yi a duniya ta yi muni, kuma mu yi iyakar ƙoƙarinmu don kawar da hakan.
 
 

4007057

 

 

 

 

 

captcha