IQNA

Sayyid Nasrullah: Manzon Allah (SAW) Ne Ya Kawo Wa Dan Adam Babban Canji Na Kamala A Rayuwa

21:44 - October 23, 2021
Lambar Labari: 3486464
Tehran (IQNA) Sayyid Hassan Nasrullah ya gabatar da jawabi a babban taron Maulidin Manzon Allah (SAW) a birnin Beirut na Lebanon.

Babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrullah ya yi bayani a wurin taron Maulidin manzon Allah (SAW) a birnin Beirut a daren jiya, inda ya bayyana cewa,  manzon Allah ya zo da canji wanda ya sauya dan adam, daga wani abu daban zuwa mutum mai kamala, inda ya dora dan adam kan turbar imani da tauhidi.
 
Baya ga haka kuma ya sauya rayuwar zamantakewa ta mutane zuwa mafi kyawun rayuwa, wadda ake kiyaye adalci da girmama dan adam a cikinta.
 
Sayyid Nasrullah ya ce manzon Allah (SAW) baya ga yaki da zalunci da kare hakkin dan adam da tabbatar da adalci a tsakanin al’umma da ya yi, ya kuma yaki nuna banbanci tsakanin bil adama, da hakan ya hada da nuna banbancin launin fata ko kabila, ko fifita masu galihu a kan marassa galihu, da dai sauran dabi’u na rashin adalci a cikin zamntakewar ‘yan adam.
 
Sannan kuma wani abu mai matukar muhimamnci a cikin zamantakewa da ya tabbatar shi ne, dawo wa mace da matsayinta na mtum a cikin al’umma, wanda kuma dukkanin wadannan muhimman ayyuka da ya gudanar, ya shinfida su ne a kan koyarwar sakonsa da ya zo da shi daga Allah, kuma dukkanin wannan gagarumin aiki da manzon Allah (SAW) ya aiwatar, ya wakana ne a cikin shekaru 23 tsakanin aiko shi zuwa wafatinsa.
 
Sayyed Hassan Nasrallah a lokacin da ya juya kan halin da ake ciki ta fuskar siyasa da tsaroa  Lebanon, ya tabbatar da cewa, a shirye suke wajen ci gaba da yin tsayin daka domin kare iyakokin kasar Lebanon da albarkatun man fetur da iskar gas na kasar, yana mai ishara da irin matakan tsokana da Isra’ila take dauka dangane da batun man fetur da iskar gas mallakin kasar Lebanon da ke cikin teku.
 
Ya ce kungiyar na ci gaba da bin diddigin bincike kan harin da aka kai wa masu zanga-zangar lumana a unguwar Tayouneh da ke beirut, kuma tana dakon sakamakon binciken, domin tabbatar da cewa an yi adalci wajen kame dukkanin wadanda suke da hannu a cikin lamarin, tare da yi musu hukuncin da ya dace da su.
 
 
https://iqna.ir/fa/news/4007167
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha