IQNA

Baje Kolin Kayayyakin Fasahar Rubutu Na Musulunci A Makon Maulidin Manzon Allah A Ankara

18:16 - October 24, 2021
Lambar Labari: 3486469
Tehran (IQNA) tun daga ranar sha biyu ga watan Rabiul Awwal aka fara gudanar da baje kolin kayayyakin fasahar rubutu da zane-zane na musulunci a birnin Ankara na Turkiya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, tun daga ranar sha biyu ga watan Rabiul Awwal aka fara gudanar da baje kolin kayayyakin fasahar rubutu da zane-zane na musulunci a birnin Ankara na kasar Turkiya.

Wannan baje koli wanda karamin ofishin jakadancin Iran a kasar ta Turkiya ya dauki nauyin shiryawa, ya samu karbuwa matuka a wajen mutanen kasar da ma masu yawan bude ido a  kasar.

A baje kolin dai ana nuna wasu daga cikin alluna da suke dauke da nau'oin ayyukan zane-zane na fasaha, da kuma rubutun ayoyin kur'ani ko addu'oi wadanda aka yi amfani da salo na musamman mai kayatarwa matuka wajen rubuta su.

 

4007500

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha