IQNA

Ana Cikin Halin Rashin Tabbas A Sudan Bayan Da Sojoji Suka Hambarar Da Majalisar Ministoci

16:14 - October 25, 2021
Lambar Labari: 3486473
Tehran (IQNA) sojojin kasar Sudan sun hambarar da majalisar ministocin kasar a safiyar yau.

Dakarun soji a Sudan sun kame wasu jami'ai da 'yan siyasa da sanyin safiyar yau Litinin, ciki har da Ministan Masana'antu Ibrahim Al-Sheikh da Gwamnan Khartoum, Ayman Nimr, kamar yadda kuma aka killace Firayi Ministan Kasar Abdallah hamdok a gidansa.
 
'Yar Ministan Masana'antu Ibrahim Al-Sheikh ta shaidawa wasu kafofin yada labarai cewa rundunar hadin gwiwa ta cafke mahaifinta daga gidansa da asubahin yau Litinin.
 
Wasu rahotannin sun sun ce an kame Mohamed Al-Faki Suleiman memba na Majalisar Sarakunan Sudan, da kuma Ministan Yada Labarai Hamza Balloul, Ministan Sadarwa Hashem Hasab Al-Rasoul da shugaban Jam'iyyar Socialist Baath Party a Sudan Ali Al-Rih Al-Sanhoury.
 
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya kuma nakalto wasu majiyoyi daga dangin Faisal Muhammad Salih, mai ba Firaiministan Sudan shawara kan harkokin yada labarai, cewa rundunar soji ta kutsa kai cikin gidansa tare da cafke shi.
 
Wasu rahotannin sun ce an katse layukan Intanet kuma sadarwa a wasu wurare a babban birnin, ya kara da cewa sojojin sun rufe gadoji da hanyoyi a Khartoum.
 
A halin da ake ciki, masu zanga -zanga sun toshe wasu hanyoyi a babban birnin kasar tare da cinna wa tayoyi wuta don nuna adawa da matakin kame-kamen da sojoji suke yi.
 
A wata sanarwa da shugaban kwamitin kungiyar ta AU, Musa Faki Mahamat, ya fitar a wannan Litini, ya nuna matukar damuwarsa akan mummunan halin da aka shiga a Sudan, bayan cafke firaministan kasar Abdollah Hamdok da kuma wasu manyan ‘yan siyasa.
 
Ya kuma bukaci a gaggauta tattaunawa tsakanin sojoji da fararen, wacce ita kadai hanyar da zata ceto kasar a cikin halin data tsunduma.
 
Yanzu haka dai an shiga zaman dar-dar a kasarta Sudan, bayan da rahotanni suka ce an yi yunkurin juyin mulki aka kuma kame mambobin gwamnatin rikon kwarya.
 
Wasu kafofin yada labarai sun rawaito Abdallah Hamdok, na mai kira ga jama’ar kasar da kada su yarda da juyin mulkin, yayin da ita ma kungiyar kwararru a kasar ta yi kira ga jama'a da su fito kan tituna domin bijirewa juyin mulkin.
 
Ita ma kungiyar kasashen Larabawa ta nuna damuwa kan abinda ke faruwa a Sudan, inda sakatare Janar na kungiyar Ahmed Aboul Gheit ya yi kira ga bangaroran da ba sa ga maciji a Sudan da su martaba yarjejeniyar da aka kulla da gwamnatin riko.
 

4007789

 

captcha