IQNA

Babban Mufti Na Quds Da Falastinu Ya Yi Kashedi Kan Take-Taken Yahudawa A Kan Masallacin Aqsa

19:30 - October 25, 2021
Lambar Labari: 3486474
Tehran (IQNA) Mufti na birnin Kudus da Falasdinu ya yi gargadi kan take-taken yahudawa a kan masallacin Al-Aqsa.

Shafin yada labarai na al-ahad ya bayar da rahoton cewa, Sheikh Mohammed Hussein Muftin Quds da yankin Falasdinu kuma kakakin masallacin Al-Aqsa, ya yi gargadi kan yunkurin gwamnatin mamaya na canza sunan masallacin Al-Aqsa ta kowace hanya, da kuma ayyukan wuce gona da iri.

Mufti na Qudus ya bayyana cewa, a wani mataki mai hatsarin gaske da jami'an gwamnatin mamaya suke dauka, sun fara shirin  maido da wata majami'ar yahudawa da ke da tazarar mita 250 daga yammacin Al-Aqsa. 

A yayin da yake ishara da hare-haren wuce gona da iri da gwamnatin sahyoniyawan suke kai wa a kan masallacin Al-Aqsa da kuma yankunan Quds, ya ce: Kara kaimi da yahudawa ke yi wajen aikata wannan ta'asa, hakan na nufin mamayewa gaba dayan birnin Quds da kuma masallaci mai alfarma, da nufin ruguza masallacin alkiblar musulmi ta farko.

Muftin Quds ya yi Allah wadai da matakin da kungiyoyin yahudawan sahyoniyawan suka dauka na shiga masallacin Al-Aqsa ba bisa ka'ida ba, karkashin jagorancin wasu malaman yahudawan  masu tsattsauran ra'ayi.

4007983

 

 
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha