IQNA

Pakistan Ta Yi Allawadai Da Rusa Masallatan Musulmi A Kasar India

19:32 - October 30, 2021
Lambar Labari: 3486492
Tehran (IQNA) Gwamnatin Pakistan ta yi kakkausar suka kan lalata masallatai da wuraren ibada da dukiyoyin musulmi a Indiya.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Pakistan Asim Iftikhar Ahmad ya bayyana a cikin wata sanarwa a ranar Juma'a 28 ga watan Nuwamba cewa, Islamabad ta yi Allawadai da lalata masallatai, gidaje da shagunan musulmi a jihar Tripura ta Indiya da kungiyoyin 'yan ta'adda "Hindu Tawa" suka yi.

Ya ce gwamnatin Indiya ba ta yi nasarar ceto musulmi ba, yana mai cewa ana ci gaba da kai hare-hare a Tripura tun makon da ya gabata.

A yayin da yake kira ga kasashen duniya da su taka rawa wajen ganin an dakile karuwar kyamar Musulunci a Indiya, musamman hare-haren da ake kai wa musulmi, Ahmed ya yi kira ga kasashen duniya da su tabbatar da tsaron musulmin Indiya tare da kare wuraren ibadarsu.

A wata sanarwa da kungiyar kare hakkin jama'a APCR ta fitar a ranar 27 ga watan Oktoba, ta bayyana cewa akalla masallatai 16 ne kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayin addinin Hindu suka lalata tare da kona gidaje da shaguna na musulmi a Tripura.

 

4009098

 

 

captcha