
Rahotanni daga Afirka ta kudu an cewa, Jikan Mandela Inkosi Zwelivelile Mandla Mandela na goyon bayan a kwace kujerar da aka baiwa Isra'ila a cikin kungiyar tarayyar Afirka.
Ya kara da cewa: "Mun goyi bayan wannan bukata, domin tsarin bayar da wakilci ga Isra'ila a tarayyar Afirka abin takaici ne, kuma Musa Faki, shugaban hukumar Tarayyar Afirka, ya yi hakan ne ba tare da tuntubar kasashe mambobin kungiyar ba, ko kuma shugabannin zartarwa na kungiyar Tarayyar Afirka.
Ya ce; "Ba zato ba tsammani, ita kanta Afirka, wadda ta sha fama da mulkin mallaka da wariya da zalunci na tsawon shekaru aru-aru da kuma mamaya, a lokaci guda kuma Afirka ce za ta amince da ci gaba da mamayar da Isra'ila ke yi wa yankunan Falasdinu, da kuma tauye hakkin bil adama na Falasdinawa, da kuma ci gaba da fadada matsugunan da gwamnatin Isra'ila ke yi ba bisa ka'ida ba.
4010034