
A cewar wani rahoton The Asian Banker, wani bangare na Financial Times, da ke buga labaran kudi na duniya na wata-wata da jerin manyan bankunan duniya a kowace shekara, Bankin Al-Rajhi na Saudi Arabia Yana a matsayin bankin Musulunci mafi girma kuma mafi karfi a duniya.
Bankin yana da kadarori na dala biliyan 125 a shekarar 2020, sannan kuma Jimlar kadarorin manyan bankunan Musulunci 100 a duniya a shekarar 2020 sun karu da kashi 12%.
Manyan bankunan Musulunci guda 10 sun hada da uku daga Saudiyya, uku na Qatar, biyu na Turkiyya da daya na Kuwait da Pakistan. Bankin Al-Rajhi yana da alaka mai ƙarfi da yawancin cibiyoyin hada-hadar kasuwanci da kudade, kuma ya sami ci gaba da kashi 22% a ɓangaren kadarorin.
Bankin Musulunci na Qatar (QIB) shi ma ya zama banki mafi karfi na Qatar kuma bankin Musulunci na biyu mafi karfi a duniya a jerin bankunan Asiya a shekarar 2021.
Bankin Mizan na Pakistan, da Bankin Islama da kuma May Bank of Islam na Malaysia, su ne manyan bankunan Musulunci guda uku a gabashin Asiya.
A cikin kididdigar Cibiyar Bankin Asiya ta bana, an duba bankunan ne daga kasashe 25.
Ana kimanta ayyukan bankunan ta hanyar muhimman bayanai guda shida, gami da ma'aunin kadarorin bankunan zuwa ma’aunin babbar hajar cikin gida (GDP) da ajiyar kuɗi, gami riba a kudaden bankuna.