IQNA

Kungiyar Kasashen Larabawa Ta Soki Shugaban Isra'ila Kan shiga Masallacin Annabi Ibrahim (AS) Da Ya Yi

15:59 - November 29, 2021
Lambar Labari: 3486619
Tehran (IQNA) kungiyar kasashen larabawa ta soki shugaban Isra'ila kan shiga cikin masallacin Annabi Ibrahim (AS) da ya yi.

Kungiyar kasashen Larabawa ta yi Allawadai da shiga masallacin Annabi Ibrahim (AS) da ke garin Khalil a Falasdinu da aka mamaye wanda shugaban haramtacciyar kasar Isra’ila Isaac Herzog ya yi a jiya Lahadi.

Kamfanin dillancin labaran WAFA a Palestine ya bayyana cewa kungiyar ta ce shigar Isaac Herzog masallacin keta hurumin musulmi da kiristocin Falasdinawa ne kuma yin hakan yana daga cikin shirin yahudawan na yahudantar da wuraren masu tsarki na musulmi da kirista a Falasdinu ne.

Tun shekara 1994 wani bayahude ya kashe Falasdinawa 29 a cikin masallacin, sannan suka ware wani bangare na masallacin don bautar yahudawa, a ranakun bukukuwan Hanukkah na yahudawan, wanda ya fada a wannan shekara a jiya Lahadi.

Sojojin yahudawan sun hana Falasdinawa zuwa yankin sun kuma jibge jami’an tsaro masu yawa a dai da- lokacinda Isaac Herzog yake bauta irin ta yahudawa a cikin masallacin.

 

4016976

 

 

captcha