IQNA

15:29 - December 02, 2021
Lambar Labari: 3486632
Tehran (IQNA) Babban zauren Majalisar Dinkin Duniya, ya amince da kudurori guda uku kan warware batun Palastinu da babban rinjaye, da kuma bukatar gwamnatin sahyoniyawa ta janye daga yankunan da ta mamaye, da kuma matsayin birnin Kudus da ta mamaye.

Shafin yanar gizo na Majalisar Dinkin Duniya ya bayar da rahoton cewa, An zartas da kuduri na farko da kuri'u 148 da suka amince, yayin da 9 suka nuna adawa ciki har da Amurka da Isra’ila, 14 suka ki kada kuri’a.

Kudiri na farko ya jaddada bukatar kiran taron kasa da kasa domin inganta batun samun zaman lafiya mai dorewa, tsakanin bangarorin Palasdinu da Isra'ila.

Kudurin ya kuma yi kira ga gwamnatin yahudawan sahyoniyawan da ta mutunta dokokin kasa da kasa da kuma kaurace wa daukar duk wani mataki na yin gaban kanta a yankunan Falastinawa da ta mamaye, ciki kuwa har da gabashin birnin Kudus.

Kudirin ya jaddada bukatar gwamnatin sahyoniyawan ta janye gaba daya daga yankunan da ta mamaye a shekara ta 1967, wanda shi ma ya hada  har da gabashin birnin Kudus, da kuma samar da mafita ta adalci kan halin da 'yan gudun hijirar Falasdinu ke ciki.

An zartas da kuduri na biyu kan gabashin birnin Kudus da kuri'u 129, 11 sun nuna adawa ciki har da Amurka da Isra’ila, yayin da 31 suka ki kada kuri’a.

Har ila yau kudurin ya jaddada rashin halascin duk wani mataki na gwamnatin Isra’ila a yankunan da ta mamaye domin aiwatar da dokokinta da kuma iko da birnin Quds.

Kudirin ya kara da cewa irin wadannan ayyuka ba su da amfani kuma ba su kan ka'ida, kamar yadda kuma Isra’ila ba ta da hurumin yin hakan.

Kudiri na uku ya kuma jaddada wajabcin mutunta wurare masu tsarki na Kudus da hadin gwiwar dukkanin bangarorin don dakile duk wani tashin hankali.

 

4017906

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: