
Shafin yada labarai na Al-ahad ya bayar da rahoton cewa, tawagar kwallon kafar Aljeriya ta lashe wasan farko na gasar cin kofin kasashen Larabawa da Qatar ta karbi bakuncinsa a yammacin ranar Asabar, inda ta doke Tunisia da ci biyu.
Kocin tawagar 'yan wasan kasar Aljeriya Majid Bougreh ya mika wa al'ummar Falasdinu nasarar da suka samu a wasan, inda ya ce hakan abin alfahari ne a ga al'ummar Aljeriya baki daya.
A yayin gasar, dukkanin magoya bayan kungiyoyin kwallaon kafar na kasashen biyu Aljeriya da kuma Tunisia, sun yi ta rera take nuna goyon bayansu ga al'ummar Falastinu, a matsayin sako na nuna rashin amincewa da kulla alaka da gwamnatin yahudawan Isra'ila da wasu gwamnatocin kasashen larabawa suke ta hankoron yi.
Bayan kammala wasan dukkanin mahalarta wurin sun yi ta rera taken nuna goyon baya ga Falastinu da masallacin Quds, tare da daga tutocin Aljeriya da Tunisia da kuma Falastinu a lokaci guda.