IQNA

Wata budurwa 'yar kasar Masar ta rubuta Cikakken Al-Qur'ani Cikin Watanni 5

16:12 - December 20, 2021
Lambar Labari: 3486707
Tehran (IQNA) Fatima Youssef Adli, wata budurwa ce ‘yar kasar Masar wacce ta rubuta kur’ani mai tsarki gaba daya cikin watanni biyar.

Shafin Al-misrawi ya bayar da rahoton cewa, Fatima Yousef Adli ta ce game da ayyukanta: Na haddace kur'ani gaba dayansa ina da shekaru 15, kuma burina na rubuta kur'ani da sarrafa shi da inganta rubutun larabci.

A halin yanzu dai Fatima duk da karancin shekarunta tana shekara ta biyu a bangaren adabin harshen larabci a jami'ar azhar.

Fatima Yousef Adli ta ce "Ina zaune a kauyen Al-Haj Salam da ke Fartoush na lardin Qana, kuma a halin yanzu ina karatun adabi a shekara ta biyu a jami'ar Azhar." rubutun Larabci irin na Uthman Taha yana burge matuka, saboda haka na fara rubuta Alqur'ani mai girma a cikin wannan salon rubutun, na kammala shi a cikin watanni 5."

 

4022219

 
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha