IQNA

Gwamnatin Falastinu: Dole Ne A Yi Bincike Na Kasa Da Kasa Kan Laifukan Yakin Isra'ila

17:54 - December 21, 2021
Lambar Labari: 3486710
Tehran (IQNA) Firaministan Falasdinu Mohammad Shtayyeh ya yi kira da a gudanar da bincike kan laifuffukan yaki da gwamnatin Isra'ila ke aikatawa kan al'ummar Palasdinu.

Kamfanin dillancin labaran sputnik ya bayar da rahoton cewa, a wani taron gwamnati da aka gudanar a Ramallah, Firaministan Falasdinu Mohammad Shtayyeh ya yi kira da a bude ma'ajiyar tarihin Isra'ila ga kwamitin bincike na kasa da kasa kan kisan gillar da aka yi wa Falasdinawa a shekara ta 1948 da kuma bayan haka.

 
Ya kuma ce kashe-kashen ya lalata garuruwa da kauyuka sama da 480 tare da raba Falasdinawa sama da 900,000 da ke gudun hijira da muhallansu a lokacin.
 
Ya kara da cewa: "Isra'ila na kokarin samar da abin da take kira mafita ta hanyar shirye-shiryenta na tsugunar da 'yan gudun hijira.
 
Ya ce: "Hukumar Falasdinu ta aike da wasiku ga Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin kare hakkin bil'adama na kasa da kasa da su shiga tsakani da kuma hana yahudawa 'yan share wuri zauna cin zarafi kan Falasdinawa.
 
Ya kuma kara jaddada cewa hare-haren da yahudawa 'yan kaka-gida masu tsattsauran ke kaiwa Falasdinawa ana yin su ne tare da goyon bayan sojojin Isra'ila, musamman a sassa daban-daban na yammacin gabar kogin Jordan.
 
Mohammad Shtayyeh ya kuma yi kira ga gwamnatin Amurka da ta shiga tsakani domin ganin an ceto shirin kafa kasar Falastinu mai cin gashin kanta, yana mai cewa ya zama wajibi a koma ga cibiyoyin kasa da kasa da kuma kare tsarin samar da kasashe biyu da gwamnatin Amurka mai ci ta yi imani da shi.
 
 

 

4022417

 

 

 
 
 
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha