Tehran (IQNA) Wani jami'in gwamnatin Sana'a a kasar Yemen ya sanar da cewa, an dakatar da gudanar da aikin filin jirgin Sana'a sakamakon hare-haren da jiragen yakin Saudiyya suka kaddmar a kan filin jirgin saman na Sanaa.

Kamfanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, Kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ta sanar da cewa, bayan harin da jiragen yakin kawancen Saudiyya suka kai a filin jirgin saman birnin Sanaa a daren jiya, an rufe filin sauka da tashin jiragen saman gaba daya, sannan kuma an dakatar da dukkan jiragen agaji na MDD da sauran jiragen jin kai sauka da tashi a wurin.