IQNA

An Kubutar Da Dalibai 21 Daga Hannun 'Yan Ta'adda a Najeriya

17:29 - January 03, 2022
Lambar Labari: 3486773
Tehran (IQNA) Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara dake arewa maso yammacin Najeriya ta sanar da sakin dalibai 21 daga hannun ‘yan bindiga.

A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, Mohammad Shehu ya fitar, ya ce ‘yan bindiga da dama sun yi awon gaba da wasu ‘yan Najeriya da suka hada da dalibai da dama a ranar Juma’a a jajibirin sabuwar shekara, inda suka tare masu tafiya a kafa.
 
Ya kara da cewa: ‘Yan sanda sun samu nasarar sako dalibai 21 da aka sace bayan sun harbe ‘yan bindiga.
 
Da misalin karfe 10 na dare agogon GMT, mazauna wani kauyen da ke kusa da babbar hanya a jihar Zamfara, sun nemi taimakon ‘yan sandan yankin, inda suka bayyana cewa wasu ‘yan bindiga sun kawo cikas a kan hanyar, sun tare motocin bas guda biyar, daya daga cikinsu na dauke da dalibai. 
 
‘Yan bindigar sun kuma yi awon gaba da wasu fasinjoji da suka hada da malami da direban bas, kamar yadda ‘yan sandan Najeriya suka bayyana.
 
Shehu ya yi kira ga al’ummar wannan yanki da su guji tafiye-tafiye da daddare saboda yawaitar sace-sacen mutane .
 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha