IQNA

Wani Dan Shekaru 10 Ya Zama Mamba A Babbar Kungiyar Makaranta Kur'ani Ta Kasar Masar

20:51 - January 04, 2022
Lambar Labari: 3486780
Tehran (IQNA) Kungiyar masu karatu da malamai ta kasar Masar ta karrama wani yaro dan shekara 10 da ya haddace kur’ani mai tsarki yana da shekaru biyar tare da gabatar da shi a matsayin mamba mai daraja ta daya a kungiyar.

Kungiyar masu karanta kur’ani mai tsarki ta kasar Masar ta bayyana sunan Ahmed Tamer Mamdouh Mohammed, wani matashin haddar yara da kafafen yada labarai suka fi sani da “gwara”, mamba na kungiyar tare da girmamawa a gare shi.
 
Ahmed Tamer dan lardin Gabashin kasar Masar ne, kuma a gasar kur'ani ta kasa da kasa karo na 28, da aka gudanar a birnin Alkahira a watan Disamba, ya samu matsayi na biyu a fannin haddar kananan yara da karatun kur'ani.
 
Ahmad Tamer ya fara haddar alkur'ani mai girma tun yana dan shekara uku da taimakon mahaifinsa da mahaifiyarsa, sannan bayan shekara biyu da wata biyu yana da shekaru biyar da rabi ya haddace kur'ani baki daya.

4026076

 

 

captcha