IQNA

Muhamamd Sanusi Barkindo Shugaban OPEC Ya Ziyarci Hubbaren Imam Ali (S) A Najaf Iraki

18:01 - January 09, 2022
Lambar Labari: 3486797
Tehran (IQNA) Babban sakataren kungiyar kasashe masu arzikin man fetur OPEC ya ziyarci haramin Imam Ali (AS) da ke Najaf Ashraf a Iraki.

Tashar Akhbar Iraq ta bayar da rahoton cewa, Mohammad Sanusi Barkindo, babban sakataren kungiyar OPEC tare da tawagarsa sun ziyarci haramin Imam Ali (as) da ke Najaf Ashraf.

Kafin wannan lokacin dai shi ma Babban magatakardar MDD ya jaddada matsayi da mahimmancin birnin Najaf a cikin zukatan musulmin duniya.

Babban sakataren kungiyar OPEC Barkindo ya kai ziyarar kwanaki da dama a kasar Iraki inda ya gana da jami'an gwamnati da suka hada da na ma'aikatar man fetur, da ziyartar wuraren ibada da tarihi da kuma ziyartar wuraren ibada na Imamai na Ahlul bait (AS) da ke kasar.

Barkindo ya ziyarci ginin gundumar Najaf, inda ya gana da Louis Eliasser da wasu jami'an lardin, sannan ya ziyarci tsohon birnin Najaf.

Barkindo ya kuma ziyarci haramin Imam Hussain (AS) da ke Karbala a jiya, A cewar wata sanarwa da ma'aikatar man fetur ta Iraki ta fitar, Barikando ya bayyana jin dadinsa da ziyarar tasa zuwa kasar Iraki.

Mohammad Barkindo dan siyasar Najeriya ne wanda aka zabe shi a matsayin babban sakataren kungiyar OPEC karo na 28 a ranar 2 ga watan Yunin 2016. Shi ne kuma tsohon shugaban kamfanin mai na Najeriya.

زیارت رئیس سازمان اوپک از بارگاه مطهر امام علی (ع)

زیارت رئیس سازمان اوپک از بارگاه مطهر امام علی (ع)

زیارت رئیس سازمان اوپک از بارگاه مطهر امام علی (ع)

 

4027327

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha