IQNA

Rayuwar Desmond Tutu, Gwagwarmayar Yaki Da Mulkin Mallaka Da Wariyar Launin Fata

10:48 - January 18, 2022
Lambar Labari: 3486835
Tehran (IQNA) Rayuwar marigayi Arch bishop Desmond Tutu fitattcen malamin addinin kirista kuma dan gwagwarmaya mai yaki da wariyar launin fata a kasar Afirka ta kudu, kuma mai fafutukar kare hakkin bil adama a duniya.

An haifi Desmond Tutu ne a ranar 7 ga watan Oktoban  shekarar 1931, a wani gari mai arziƙin Zinari da ake kira Transvaal, dake cikin yankin Cape Town  a ƙasar Afirka ta kudu.

Ya yi karatun firamare a garin nasu, amma a lokacin karatun sakandare ya tafi makarantar sakandare da Bantu a a Johannesburg, wanda yanki ne da yake da koma baya matuka matuka a lokacin, wanda dukkanin mazana wurin bakaken fata ne wadanda basa da galihu, a kan haka yanayin karatu a wurin yana da wahala matuka, domin kuwa babu kulawa daga bangaren turawan mulkin mallaka ga mutanen yankin, amma duk da haka ya yi karatunsa a cikin irin wannan yanayin.

Desmond Tutu ya ɗauko hanyar mahaifinsa ta aikin malanta, to amma daga bisani ya dakata da aikin mallantar ko kuma koyarwa, a lokacin da aka ɓullo da wata sabuwar dokar tafiyar da ilimi a kasar Afirka ta kudu da aka yi wa laƙabi da “Bantu Education Act” a shekarar 1953.

A kan haka ne sai ya shiga aikin bushara a majami'u,  inda ya sami matuƙar goyon baya daga Turawan dake aikin bushara a wancan zamani, musamman ma goyon bayan da ya samu daga Bishop Trevor Huddleston, sakamakon yadda ya nuna ƙiyayya ga wariyar launin fata.

Ya fara karatu a makarantar ilimin tauhidi ta St. Peter a birnin Johannesburg a shekara ta 1958, inda ya zama cikin malaman cocin Angalican a shekara ta 1960.

A cikin shekara ta 1966 ya tafi birnin London na Ingila domin karo ilimin addinin kirista a darikar Angalican, inda a can ne ya kara fadada bincikensa a wannan fage, a lokacin ne kuma ya fara tunanin cewa addini zai iya taka rawa wajen yaki da wariyar launin fata, kuma daga lokacin ya fara rubuce-rubuce kan munin da ke tattare da wariyar launin fata a mahangar addinin kirista.

A cikin shaeakara ta 1975 Desmond Tutu shi ne ya zama babban limamin ɗarikar Angilika na farko baƙar fata a birnin Johannesburg dake ƙasar ta Afirka ta kudu.

Bayan shekara guda da kasancewa a wannan matsayi ne sai shugabannin Turawa fararen fata suka fara sanya ido a kansa da kuma ayyukan da yake gudanarwa, sakamakon yadda yake fitowa fili yana sukar nuna wariyar launin fata da ake nunawa bakaken fata a kasar, wadda turawa suke mulki da ita a lokacin, don haka ne ma ya zamanto mai fafutikar yaƙi da mulkin wariyar launin fata.

A lokacin da tsohon shugaban Afirka ta kudu Nelson Mandela ke zaman fursuna, Archbishop Desmond Tutu ne ya zamanto babban mai riƙe da ragamar jagorancin adawa da wariyar launin fata a kasar Afirka, wanda hakan ya kara jawo masa matsananciyar adawa daga turawa masu mulki a gwamnatin wariya ta kasar.

A cikin shekara ta 1980 an gudanar da wata gagarumar zanga-zangar nuna adawa da mulkin wariyar launin fata a kasar Afirka ta kudu, tare da yin kira da a saki Nelson Mandela da sauran dukkanin masu fafutuka da turawa suke tsare da su a gidajen kaso, wanda kuma Desmond Tutu na daga cikin wadanda shirya wannan zanga-zanga da kuma jagorantarta,  kan haka turawa suka kame shi suka jefa  a gidan kaso na wani lokaci

Yayin da Nelson Mandela ya fita daga gidan fursuna, an kafa hukumar sasantawa da bincike kan irin ta'annati da aka yi a lokacin mulki wariyar launin fata a Afirka ta kudu, an naɗa Desmond Tutu ne shugaban hukumar.

To amma kafin lokacin, a shekarar 1986, an zaɓe shi a matsayin babban Arch Bishop na birnin Cape Town, domin ya ci gaba da yaƙi da manufofin wariyar launin fata.

A watan Maris, na 1988, Arch Bishop Desmond Tutu, ya kaddamar da wani kamfe na adawa ga ‘yan mulkin wariya, don haka ya bukaci jama’a da su da su ƙaurace wa wani babban zaɓen larduna da gwamnatin shuagaba F W De Klerk ta shirya yi a lokacin.

A lokacin da Nelson mandela ya naɗa Desmond Tutu shugaban hukumar binciken gaskiya da sassantawa na Afrika ta kudu, ya yi ƙoƙarin tattaro bayanai daga jama'a daban-daban da suka bayar da bahasi gaban hukumar, to sai dai kuma a yayin da yake aikin binciken ya kamu da wani ciwon daji, to amma duk da hakan a ƙarshen rahotonsa, Desmond Tutu ya zargi akasarin shugabannin da suka yi mulki a lokacin Turawan mulkin mallaka cewar ba su bayar da bahasi na gaskiya ba a gaban hukumar, musamman ma yadda baƙaƙen fata ke nunawa a zahiri irin cin zarafin da suka fuskanta a zamamin mulkin wariya a duk lokacin da suka je bada nasu bahasin.

Arch Bishop Desmond Tutu ya zamanto masani ne kan harkokin yau da kullum da kuma siyasar duniya, kamar yadda kuma bai taba yin kasa a gwiwa ba wajen ci gaba da fafutuka wajen kare hakkokin bil adama, duk kuwa da cewa an kawo karshen mulkin wariya a kasar Afirka ta kudu, amma duk da haka hatta siyasa da suke mulkia  kasar yana taka musu burki a duk lokacin da suka yi wani abu da bai dace ba, ko kuma suka aiwatar da wani da zai tauye hakkokin ‘yan kasa.

Fafutukar Desmond Tutu ba ta takaita da kasar Afirka ta kudu ba kawai, ya kasance yana yin  gargaɗi ga wasu daga cikin shugabannin kasashen Afirka da cewa kada su  dauki salon mulkin kama karya kan al’ummomin kasashensu, su zamanto masu adalci da kaunar al’ummominsu, da kuma tabbatar da cewa sun yi aiki domin ci gaban al’ummominsu, maimakon mayar da mulkin kasashe tamkar gadon gidansu, ko kuam halasta ma kansu dukiyoyin al’ummomin kasashensu, inda Desmond ya yi imanin cewa, duk shugabannin Afirka da suke yin haka, to sun yi hannun riga da manufofi na demokradiyya da ma ‘yan adamtaka.

Irin wannan fadakarwa ta Desmond Tutu ba ta bar shugabanin ƙasashen yamma ba, don kuwa Desmond Tutu ya buƙaci Shugaba George Bush na Amirka, tare da Firaministan Birtaniya Toni Blair, da su fito su gayawa duniya sun yi kuskure sakamakon yadda suka ƙaddamar da yaƙi kan ƙasar Iraqi, yakin da ya yi sanadiyyar mutuwar da dama, da kuma zama sanadin bullar kungiyoyin ta’addanci masu hadari.

Baya ga haka kuma ya kasancea  sahun gaba wajen sukar manufofin kasashen turai ‘yan jari hujja, wadanda suke yin amfani da karfin tattalin arzikinsu wajen danne kasashe raunana ko kuma masu tasowa, tare da dora kamfanoninsu a dukkanin harkoki na wadannan kasashe, ta yadda za su rika tatsar arzikinsu hankali kwance, ba tare da wani ya isa ya daga musu kara ba, kamar yadda ta kasance ga kasar Afirka ta kudu tsawon shekaru.

Desmond Tutu bai yarda malaman addini su koma su kulle kansu a wuraren ibada ba, ba tare da sanin halin da kasarsu da al’ummarsu suke ciki ba, kamar yadda kuma bai yarda da cewa malaman addini su yi gum da bakunansu a kan harkokin da suka shafi lamurran siyasa  da kuma tafiyar da harkokin mulkin kasashensu ba, inda yake ganin cewa, malamai suna da gagarumar rawa da za su iya takawa wajen tabbatar da ganin an yi abin day a dace a cikin harkokin mulki da siyasa, ta hanyar sanya ido a kan yadda ake mulki da kuma tafiyar da siyasar kasashensu, idan an yi daidai , su karfafa shugabanni kan ci gaba da yin abin da aka yi, idan kuma ba a yi daidai ba, su fito su fada wa shugabanni gaskiya domin a gyara, idan kuma ba su gyra ba, su fili su sanar da jama’a, kuma su soki abin da ake yin a ba daidai ba a cikin harkokin mulki, wanda a ganinsa hakan yana da babban tasiri a cikin al’umma a dukkanin bangarori, domin kuwa tasirin malamai na addini tasiri ne da yake da alaka da akidar mutane da imaninsu.

Dangane da matsayarsa kan al’amarin Falastinu kuwa abu ne wanda yake a fili ga kowa a duniya, inda baya boye kalamansa na yin Allawai da ayyukan zalunci da danniya da yahudawan Isra’ila suke yi kan al’ummar falastinu, inda sau daya Desmond Tutu yana kamanta mulkin Isra’ila a kan al’ummar falastinu na mulkin wariyar launin fata na Afirka ta kudu, kamar yadda kuma wannan ita ce mahangar Nelson Mandela har ya bar duniya.

A kan haka Tutu ya sha gabatar da laccoci, inda yake sukar manyan kasashen duniya musamman ma Amurka, kna yadda suke bayar da kariya ido rufe ga ayyukan cin zalun da ake yi kan al’ummar falastinua  cikin kasarsu tag ado, inda kuma yakan bayyana mahangarsa kan yadda ya kamata a samu mafita dangane da wannan lamari, ta hanyar kafa kasashe biyu, na Isra’ila da kuma Falastinu mai cin gashin kanta, wadda ba ta a karkashin amamyar yahudawa ‘yan kaka gida, wanda a ganinsa hakan ne kawai mafita, kuma shi ne adalci.

A shekara ta 1984 ya samu kyautar Nobel ta zaman lafiya da gwagwarmayar yaki da wariyar launin fata da kuma kare hakkin bil adama.

Ya kasance daya daga cikin mutanen da ake ganin ganin girmansu matuka a kasar Afirka ta kudu, da ma sauran kasashen Afirka, da ma duniya

A ranar Lahadi 26 ga watan Disamban 2021, Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ne ya sanar da rasuwar  Desmond Tutu a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya rasu a wani asibiti dake birnin Cape Town a ranar ta Lahadi yana da shekaru 90 a duniya.

Kasashen duniya da dama da kuma fitattun mutane a duniya suna ci gaba da aikewa da sakon ta'aziyyarsu kan rasuwar Archbishop Desmond Tutu.

Majalisar musulmin kasar Burtaniya ta fitar da bayanin da ke cewa, Desmond Tutu mutum ne wada tarihi ba zai taba mantawa da shi ba, sakamakon gagarumar gudunmawar da ya bayar a cikin rayuwarsa, inda baya ga gwagwarmaya da wariyar launin fata da ya yi tare da abokinsa Nelson Mandela, ya kuma kasance daga cikin mashahuran mutane a duniya da suke kare hakkin bil adama ba tare da la’akari da addini ko kabila ba, inda suka bayar da misali kan yadda ya kasancea  gaba wajen kare hakkokin musulmi na Falastinu da Iraki da Myanmar da makamantansu, wanda a cewar bayanin majalisar musulmin kasar ta Burtaniya, Desmond Tutu gwarzo ne na dukkanin raunana da duk wadanda ake zalunta a duniya.

 

By: Abdullahi Salihu Usman   (IQNA)

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha