IQNA

Musulmin Burtaniya Na Aiwatar Da Wani Shiri Na Taimaka Ma Mabukata A Kasar

18:14 - January 22, 2022
Lambar Labari: 3486851
Tehran (IQNA) Masallatai biyu a birnin Birmingham na kasar Ingila suna raba buhunan abinci ga mabukata a daidai lokacin da lokacin sanyi ke kara tsanata da kuma tsadar makamashi.

Shafin Birmingham Mail ya bayar da rahoton cewa, yayin da iyalai a Biritaniya ke fama da matsalar tsadar rayuwa, masallata a birnin na Birmingham suna kai buhunan abinci ga mutane mabukata.

Masallacin Green Lane da ke yankin Small Heath da Masallacin Al-Fallah da ke Handsworth ne suke hada taimakon daga musulmi da suke bayar da gudunmawa, da hakan ya hada da abinci da kuma kudade da sauran kayayyakin bukatar rayuwa.

Kungiyar agaji ta Islamic Relief ta Burtaniya ta hada hannu da masallatai domin samar da buhunan abinci ga mabukata, wanda kuma a ranakun jiya Asabar 21 ga Janairu da kuma yau 22 ga wata ne ake tattara taimakon da kungiyar ta bukata daga musulmi.

Tufayl Hussein, darektan kungiyar agaji ta Islamic Relief ta Burtaniya ya ce Masallatai suna gudanar da ayyuka masu ban mamaki kuma za su ba da taimako da tallafi da ake bukata ga marasa marasa galihu musamman ma wadanda ba su da wurin zama da suke rayuwa a waje da suke cikin mawuyacin hali.

Ya ce taimakon da musulmi suke bayarwa a Burtaniya dai ya hada kowa da kowa, ba tare da la’akari da addini ko kabila ba, ana bayar das hi ga duk wani mabukaci, kamar yadda musulunci ya yi umarni.

4030395

 

 

 

captcha