IQNA

15:38 - January 25, 2022
Lambar Labari: 3486864
Tehran (IQNA) Jami'an Aljeriya sun gargadi 'yan kasarsu game da yiyuwar yin kutse cikin wayoyinsu tare da kwasar bayanai na sirri, ta hanyar manhajar Isra’ila, biyo bayan dagewar da kasar ta yi na kin yin sulhu da gwamnatin Isra’ila.

Hukumomin kasar Aljeriya masu alaka da hanyoyin sadarwa na zamani sun aike da gajerun sakonni ga masu wayoyin hannu, inda suka bukaci su yi taka tsantsan wajen tunkarar sakwannin da ba a san sunansu ba, ta yadda ba za a iya yin leken asiri ba.

Jami'an Aljeriya sun ce hakan na iya haifar da satar bayanai kai tsaye daga wayoyin jama’a.

Jaridar Al-Shorouk ta kasar Aljeriya ta bayar da rahoton cewa, akwai bayanai da dama game da kai hari ta hanyar yanar gizo kan 'yan kasar Aljeriya ta hanyar shirye-shiryen leken asiri na dijital na yahudawan Isra’ila da kasar Maroko ke amfani da su.

Rahotanni sun ce sakonnin sun zo ne daidai da wani jerin sunayen da jaridar Haaretz ta Isra'ila ta fitar, wanda ke cewa a cikin tsarin an tabbatar da jerin sunayen duk wadanda shirin leken asirin na Pegasus ya shafa, da kwararru kan harkokin yada labarai, baya ga Larabawa masu fafutukar siyasa da kare hakkin bil'adama.

Jaridar Al-Shorouk ta bayyana yadda takun saka tsakanin Maroko da Aljeriya ke kara tabarbarewa a matsayin dalilan yiyuwar yin leken asiri kan wayoyin hannu na ‘yan Aljeriya.

 

4031281

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: