IQNA

21:36 - January 26, 2022
Lambar Labari: 3486872
Tehran (IQNA) Masallacin Esteghlal shi ne masallaci mafi girma a kudu maso gabashin nahiyar Asiya, wanda ke a dandalin Mardika a birnin Jakarta, babban birnin Indonesia.

Masallacin Esteghlal shi ne masallaci mafi girma a kudu maso gabashin nahiyar Asiya, wanda ke a dandalin Mardika a Jakarta, babban birnin Indonesia, wanda tun daga hasumiyarsa zuwa ginshiƙai da adon bango, alamomin Alƙur'ani da ke cikin zayyana wannan masallaci suna kayatar da idanu ga maziyarta.

Masallacin Esteghlal na Jakarta shi ne masallaci mafi girma a kudu maso gabashin Asiya ta fuskar kawun aiki, an sanya wa masallacin suna “Esteghlal” ne saboda an fara gina shi ne bayan da Indonesiya ta samu ‘yancin kai daga kasar Holland a shekarar 1949, lokacin da aka yi kokarin gina babban masallacin da ya cancanci Indonesiya a matsayin kasar Musulunci mafi girma.

Masallacin Esteghlal yana da fadin murabba'in mita 2,750 kuma tsayinsa ya kai mita 33, kuma yana da fadin da mutane 200,000, za su iya yin salla a cikinsa a lokaci guda, ya zama masallaci mafi girma a kudu maso gabashin Asiya.

An yi amfani da fasahar ginin hasumiya na Italiyanci wajen zayyana da kuma kawata hanyar wannan masallaci.

Har ila yau, dardumomin da ake amfani da su wajen yin salla a wannan masallaci a kasar Turkiyya ake yin su.

Wannan masallaci yana da kofofi guda bakwai kuma kowanne daga cikin kofofin bakwai sunanta daga cikin sunayen Allah ne.

Lamba bakwai kuma yana wakiltar sammai bakwai a ilmin falaki na sararin samaniya na Musulunci.

 

4031472

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: