
Jaridar Free Press Journal ta bayar da rahoton cewa, Malala Yousafzai, wadda ta lashe kyautar zaman lafiya ta Nobel a shekarar 2014, kuma mai fafutukar kare hakkin mata, ta yi kira ga shugabannin Indiya da su kawo karshen mayar da mata musulmi saniyar ware saboda sanya hijabi a makarantun kasar.
An fara muhawarar hijabi ne a watan Janairu a kwalejin jihar PU da ke Orenopi, a cikin jihar Karnataka, inda aka bukaci dalibai shida sanye da hijabi da su fice daga harabar makaranta.
Yanzu haka lamarin ya yadu zuwa sassa daban-daban na jihar, yayin da kuma matasan mabiya addinin Hindu ke gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewa da sanya hijabi tare da nuna goyon baya ga masu tsatsauran ra’ayi.
Batun ya bazu zuwa jihar Madhya Pradesh da Podocher, wanda 'yan siyasa 'yan jam'iyyar BJP ne ke mulki. Wani minista a Madhya Pradesh ya yi kira da a dauki matakai na tilasta dalibai sanya tufafi iri daya ta hanyar hana wasu sanya hijabi a makarantun kasar.
Da take mayar da martani kan lamarin, Malala ta rubuta a shafinta na Twitter cewa: "Abin takaici ne a hana 'yan mata masu hijabi shiga makarantar, ta ce dole ne shugabannin Indiya su daina mayar da mata musulmi saniyar ware a cikin kasarsu, domin kuwa su ba baki ba ne a cikin kasarsu ta gado.