IQNA

Dan wasan Manchester United Ya Nuna Goyon Bayansa Ga Mata Musulmi Masu Saka Hijabi A India

22:41 - February 10, 2022
Lambar Labari: 3486936
Tehran (IQNA) Tauraron kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ya yi magana a kan yadda ake cin zarafin mata musulmi daliban kasar Indiya masu lullubi a shafinsa na Instagram.

Jaridar New Indian Express ta bayar da rahoton cewa, "Paul Pogba ya watsa wani faifan bidiyo a shafinsa na Instagram inda ya ce mabiya addinin Hindu na tursasa 'yan mata musulmi masu sanye da hijabi don shiga jami'o'i a Indiya."

Pogba wanda yake da mabiya sama da miliyan 51 a Instagram, ya bayyana abin da ake yi wa mata musulmia  India a matsayin take hakkokinsu na addini da kuma 'yan adamtaka.

An fara muhawarar hijabi ne a watan Janairu a kwalejin jihar PU da ke Orenopi, a cikin jihar Karnataka, inda aka bukaci dalibai shida sanye da hijabi da su fice daga harabar makaranta.

Yanzu haka lamarin ya yadu zuwa sassa daban-daban na jihar, yayin da kuma matasan mabiya addinin Hindu ke gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewa da sanya hijabi tare da nuna goyon baya ga masu tsatsauran ra’ayi.

Batun ya bazu zuwa jihar Madhya Pradesh da Podocher, wanda 'yan siyasa 'yan jam'iyyar BJP ne ke mulki. Wani minista a Madhya Pradesh ya yi kira da a dauki matakai na tilasta dalibai sanya tufafi iri daya ta hanyar hana wasu sanya hijabi a makarantun kasar.

 

4035477

 

captcha