IQNA

Gagarumin maci a Yemen bayan cikar shekaru 7 da Saudiyya ta fara kaddamar da yaki kan kasar

20:21 - March 26, 2022
Lambar Labari: 3487092
Tehran (IQNA) A yau ne al'ummar kasar Yemen suka shiga shekara ta takwas na hare-haren wuce gona da irin na kawancen Saudiyya da Amurka, inda suka gudanar da gagarumin zanga-zangar nuna jajircewarsu wajen ganin sun 'yantar da duk wani taki na kasarsu.

A rahoton tashar al-Masira, a yau ne al'ummar kasar Yemen suka shiga shekara ta takwas na hare-haren wuce gona da irin na kawancen Saudiyya da Amurka, inda suka gudanar da gagarumar zanga-zangar nuna jajircewarsu wajen ganin sun 'yantar da duk wani taki na kasarsu.

Tashar Al-Masira ta bayar da rahoton cewa, al'ummar kasar a larduna daban-daban sun gudanar da maci a jiya domin tunawa da gwagwarmayar kasa da kuma cika shekaru bakawai da sojojin kawancen Saudiyya da Amurka suka kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan kasar Yemen.

Mahalarta tarukan on sun yi ta rera taken nuna goyon baya ga 'yanci da tsayin daka wajen fuskantar 'yan ta'adda, tare da rike  tutocin kasar Yemen da hotunan jagoransu shahidan Sayyid Hussein Badraddin da kuma jagoran juyin juya halin kasar Yemen Sayyid Abdul Malik Badraddin Alhuthi.

Har ila yau gwamnan Sa’ada Mohammed Jaber Awad ya jaddada a cikin jawabinsa cewa, Amurka c eke yaki da al’ummar kasar Yemen, amma karnukan farautarta ne suke aiwatar mata da hakan a aikace.

 Dukkanin bayanan da aka gudanar a gangami da tarukan da a ka yi jiya a Yemen, sun jaddada cewa, babu gudu babu ja da baya wajen kare kasar da martabarta, da kuma ci gaba da yin turjiya a gaban ‘yan mamaya, tare da mayar da martani da duk abin da ya sawaka a kansu.

 

 

 

 

 

https://iqna.ir/fa/news/4045096

Abubuwan Da Ya Shafa: tsayin daka
captcha